YAN’ UWANTAKA A MUSULUNCI:

DAGA MABUKACIN RAHAMA WAJEN MADAUKAKIN SARKI ALLAH

 

  ADAM IDRIS USMAN

(ABUL HAFEEZ)

 

A WAJEN TARON TARBIYYA NA DALIBAI

 

WANDA YA GUDANA

A

 

MAKARANTAR SARAUNIYA AMINA (QUEEN AMINA) DAKE

KADUNA

 

28TH AUGUST 2015

 

Abubuwan da za mu tattauna akan su:

FALALAR YAN’UWANTAKA

LADUBBAN YAN’UWANTAKA

HAKKOKIN DAN ‘UWA

HANYOYIN KARFAFA YAN’UWANTAKAR ISLAMA

CIKASAWA

Gabatarwa:

Kalmar “Ukhuwwah”  wadda da hausa ita ce Yan uwantaka, sananna ce ma’anar ta: wanda kuka hada alaka da shi ta jini, amma “Ikhwan”  tana daukar  aboki a cikin kowace mu’amala ta rayuwa.

Ibn Abi Haatim yana cewa: “Mutanen Basrah sun taru akan cewa “Ukhuwwah” suna ne da ake nufin dangi na jini da shi, amma Lafazin “Ikhwan” ana nufin abokin mu’amala” (lisanul Arab: 14/19).

yan’ Uwantaka a wajen malamai: itace tarayyar wani mutum da wani wurin haihuwa ko shayarwa,  amma ana iya aron Kalmar don amfani da ita ga dukkan abokin tarayya a qabila ko addini ko sana’a ko wata mu’amala ta soyayya ko wanin ta” ( Mufradat Arragib:7/317)

Ibn Hajar Al- asqalaaniy Yayi bayani game da fadin Allah: “Lallai Muminai Yan’ Uwan Juna ne” yace: “abun nufi wajen son junan su zuwa ga gamammen kira”. ( Fathul Baariy: 7/317).

Imamul Manaawiy yace: “Dan’ Uwa: shine wanda ya bubbugo tare da dan’ Uwan sa daga mabubbuga daya ta kowace fuska” (Attauqeef Alaa Muhimmaat Atta’areef,p:4)

Haka Imamaul Kafawiy ya nuna a cikin littafin sa Alkulliyaat shafi na sittin da uku.

 • FALALAR YANUWANTAKA
 1. Yan’Uwantaka tana da falala mai yawa, daga ciki akwai:
 2. karfafa ginshikin Musulunci: Son Dan’ uwa ga Dan’ Uwan sa yana daga mafi karfin ginshikin Musulunci, Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sun Tabbata a gare shi yace: “ mafi karfin ginshikin Musulunci shine jibantar al’amura don Allah, da kiyayya don Allah, da so don Allah da fushi don Allah” ( silsilatul Ahaadith As- swaheehah, imamul Albaniy: 992. Sharhhus Sunnah, Imamul Bagawiy:3468. Addabraaniy: 125.)
 3. Allah yana son wadanda sukai soyayya don shi: Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sun Tabbata a gare shi yace: “Allah – mai girma da daukaka – yace: soyayya ta ta tabbata ga wadanda suka yi soyayya don ni ”( Imamu Ahmad:233, 247, Albaaniy fi Swaheehil Jaami’I 4331)
 4. Yan Uwantaka na dandanawa mai yin ta zaqin Imani: Abu Hurairah yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “wanda yake son ya sami zakin Imani sai yaso wani ba tare da wani dalili ba sai don Allah mai girma da daukaka” ( Swaheehul Jaami’i: 6164)
 5. Zama akan karagu na zinari ranar Alqiyama: Abdullahi bin Abbas yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata A gare shi yace: “ Allah mai girma da daukaka yace: masu soyayya don ni suna da karagu na haske wanda har Annabawa da shahidai suna burin samun sa” (Swaheehul Jami’i: 4312)
 6. Mafi girman daraja a wurin Allah wanda yafi son dan Uwansa: Ibnu Amr yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata A gare shi yace: “ mafi alhairin Abokai a wurin Allah mafi Alhairin su a tsakanin su” (Swaheehul Jami’i: 3270)
 7. Soyayya don Allah na daga cikin Imani: Abu Hurairah yace: Manzon Allah tsira da Amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “ ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, ba zaku yi Imani ba har sai kuna son junan ku, shin kuna son in yi muku nuni da abun da idan kuka aikata shi zaku so junan ku? Ku yada sallama tsakanin ku” ( Muslim:54)
 8. Mutum ranar qiyama ana ta da shi da wanda yake so: An samo Hadisi daga Anas dan Malik, lallai wani Mutum ya tambayi Manzon Allah akan tashin Qiyama, sai Manzon tsira da Aminci yace masa me ka tattala mata? Sai yace: babu komai sai dai ni ina son Allah da Manzon sa, sai Manzon Allah yace Masa: “ kai kana tare da wanda kake so”
 9. Anas yace: ba muyi farin ciki ba, fiye da fadin Manzon Allah kai kana tare da wanda ka keso, Anas yace: ni ina son Manzon Allah da Abubakar da Umar, kuma ina fatan in kasance tare da su duk da ban yi aiki irin nasu ba.
 • LADUBBAN YANUWANTAKA
  1. Ladubban Yan’uwantaka suna da yawa, wanda suka hada da:
 1. Yin Yanuwantaka don Allah kawai: Yan’Uwantaka don Allah tana kasancewa karbabba a wajen Allah matukar ba anyi ta don tunanin wata fa’ida ta duniya ba, sai dai kawai an yi ta don Allah ne. Manzon Allah (S.A.W) yace: “duk wanda yake son ya dandani zaqin Imani to yaso Mutum, soyayya don Allah kawai”
 2. Zabar Abokin zama: lallai ne zaben Aboki yana da girman gaske a cikn Addinin Islama, domin ba kowane mutun ake Abota dashi ba, Manzon Allah (S.A.W) yace a Hadisin Abu Huraira “ lallai mutum yana kan Addinin Abokin sa don haka dayan ku ya duba wa zai yi abota da shi” ( Imam Ahmad: 7212, Abu daud: 4833, tirmidhi: 2387, Albaniy fes- swaheehah:927)
 3. Kuma Manzon tsira yace: “kada kai abota da kowa sai Mumini kuma kada kowa ya shiga gidan ka sai mai tsoron Allah” ( Imamn Ahmad:3/380, Imam tirmidhi:2395, Albaniy swaheehul Jaami’i:7341)

Malamai sun ce lallai wanda za kai abota dashi ya cika siffofi biyar kamar haka:                                                                                                                 1. Ya zama mai hankali ba mahaukaci ba:

wajibi ne  wanda zai zama abokin ka ya zama mai hankali, ba mahaukaci ba, ba fasiki ko wawa ba, domin fasiki ya yi kama da macijiya wadda ba’a samun komai a tare da ita sai cizo ko dafi. (Raudatul Uqala’i)

 1. ya zama mai kyawawan dabi’u:

Ibn Hibban yana cewa: lallai mai hankali kada yayi abota da kowa sai mai kyakkyawan ra’ayi, mai Ilimi da Addini, domin hakan yana nuna kai mai hankali ne. akwai wani tsohon Karin Magana da ke cewa “gaya mun abokin ka sai in gane kai waye (show me your friend I tell you who you are)”

 1. kada ya zama mai son duniya:

Allah ta’ala yana cewa: “ ka kau da kai daga wanda ya juya baya daga ambaton mu bai nufin komai sai rayuwar duniya” Suratun Najmi: 29

Mai kwadayin duniya bai taimaka maka da komai sai halaka da tabewa ta hanyar sai da addinin ka don wani dan burin duniya wanda zai kare.

 1. kada kayi abota da dan bid’ah:

Malamai sun ce da kai abota da dan bid’ah gara kayi abota da mai sabon Allah iya rayuwar ka, Sa’eed bun Jubair yana cewa: “da nayi abota da fasiki dan fashi amma mai bin sunnah yafi soyuwa gare ni da nai abota da dan bid’ah mai yawan ibada” ( Ibn Battah, Al-Ibanah Asswugrah: 132)

 1. kada aboki ya zama mai bayyana fasikanci ba tareda kunya ba.
 2. HAKKOKIN DAN ‘UWA
 • Nuna wa Dan ‘uwa damuwa ya yin shiga kowane hali a rayuwa kamar yin tarayya da shi yayin farin ciki da yayin bakin ciki
 • Taimakon sa da dukiya, wannan yana kan matakai uku kamar:
 1. taimaka masa da abun da yai saura na bukatun ka don ka share masa hawayen sa, kuma baka bukatar sai ya roke ka
 2. ajiye shi daidai da kai yayin bukata, kamar yadda kake wa kan ka haka kake masa komai, baka fifita kan ka akan sa
 3. fifita shi akan ka yayin bukata, kamar yadda sahabbai suke yi
 • Taimakon sa wajen basa bashi yayin bukata, ko ka biya masa bashin da ya kasa biya, Abu Busrin ya ruwaito daga Manzon tsira cewa: “wanda ya taimaki wanda ke cikin qunci ko ya biya masa bashin sa, Allah zai saka shi a inuwar sa ranar da babu wata inuwa sai inuwar sa”
 • Gaishe shi yayin rashin lafiya, Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “duk wanda ya gaida mara lafiya ba zai gushe ba yana kan tafarkin Aljanna ko fiffiken ta”( Muslim: 2568
 • Tsare masa sirrin sa, Jabeer dan Abdullah ya ruwaito daga Manzon tsira yana cewa: “Idan mutum ya baiwa dan uwan sa wani labari sannan ya juya baya, to – labarin- ya zama Amana” Abu daud: 4868).
 • Cika alkawarin sa, yana daga siffar muminai suna cika alkawari idan sun kulla kamar yadda Allah ya bayyana a cikin suratul Baqara, domin yana daga alamar munafunci kin cika alkawari kamar yadda manzon Allah yake cewa: “yana daga Alamar munafiki guda uku: idan yazo bada labari sai yai karya, idan yai Alkawari ya saba, idan an amince masa yai yaudara”
 • Karbar Uzurin sa da yarda da abun ya fadi
 • Yin nasiha ga Aboki yayin bukatar hakan, domin manzon Allah yana cewa: “hakkin muslmi akan musulmi shida ne”:
 1. Idan ya hadu dashi yai masa sallama
 2. Idan ya gayyace shi ya amsa masa
 3. Idan ya bukaci adduar sa yai masa
 4. Idan yai atishawa yai masa Addua
 5. Idan yai ciwo ya gaishe shi
 6. Idan ya rasu ya bi gawar sa
 • Yin nasiha a boye ba da niyyar tozarci ba
 • Kare shi daga suka ko batanci ko halaka gwargwadon iko
 1. HANYOYIN KARFAFA YANUWANTAKAR ISLAMA

Lallai Addini ya baiwa yan’uwantaka kulawa ta musamman inda ya sanya hanyoyin kyautatuwar ta da dama, kadan daga ciki sun hada da:

1.Yada sallama:  lallai yana daga abun da ke karfafa yan’uwantakar Islama, ya kara son juna, yaada sallamar Islama tsakanin musulmai, kamar yadda yazo cikin Hadisin Abu Huraira (R.A) Manzo Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “ba zaku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za kuyi Imani ba har sai kuna son junan ku, shin ba nayi muku nuni ga wani abu ba wanda idan kuka aikata shi za ku so junan ku? Ku yada sallama a tsakanin ku” (muslim:54)

 1. Musafaha: lallai yin musafaha da juna tana haifar da dankon soyayya tsakanin yan’uwa, bayan abun da ke cikin ta na lada mai girman gaske, kamar yadda a hadisin Barra’u dan Azib yace Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yace: “babu wasu Musulmai guda biyu da zasu hadu da juna suyi musafaha face an gafarta musu kafin su rabu da juna” ( Abu Dawua:5212, tirmidhi:2727, Albaniy fe swaheehil jaami’i:5777
 2. Nuna soyayya da tausayawa juna: don fadin Manzon Allah (S.A.W): “misalin Muminai wajen soyayyar su da tausayin junan su da tausasawar su, kamar misalin jiki ne, idan wata gaba tai ciwo daga gare shi dukkan sauran jikin sai gume da zazzabi da rashin barci” (Bukhariy:6011, Muslim:2086)
 3. Yiwa juna kyauta

Yin hakan yana da tasiri mai girma a musulunci, kuma yana haifar da kauna da soyayya tsakanin masoya

 1. Fada masa kaunar sa: Bada labarai ga wanda kake so cewa kana son sa, domin hakan yana daga cikin sunnah
 2. Nuna kan kan da kai ga juna: ba tareda nuna girman kai ko fifiko ga juna ba
 3. Yawan ziyartar juna: domin mai ziyara hatta mala’iku suna neman masa gafara, kuma yana kan tafarkin Aljannah har ya dawo
 4. CIKASAWA:

lallai Yan uwantakar Islama girman matsayin ta ya wuce dukkan wata Yan’ uwantaka a duniya, domin tana dauke da tausasawa, tausayawa, yafiya, taimakon juna, sannan kuma kare mutunci, dukiya da jinin juna daga dukkan sharri.

Don haka wajibi ne a gare mu mu zama masu bin karantarwar Islama don neman tsira duniya da lahira.

Allah muke roko ya karfafa yan’uwantakar mu akan abunda yake so kuma ya yarda da shi.

Wal hamdu lillaahi rabbil Aaalameena

Adam Idris Usman (Abul Hafeez)

www.asnim.org.ng

info.adamidris.asnim@yahoo.com

abidaayah@gmail.com

albidaayah@rocketmail.com

adamidris@facebook.com

whatsapp no:08024367278

Adam Idris Usman